Showing 1 words to 791 words out of 791 words

Chapter 1 - HAMADA BOOK 1 PART 1 HAUSA NOVEL

26 Feb 2025

1431

HAMADA BOOK 1 PART 1



HAMADA-1
ARAJ! HARAJ!! HARAJ!!!" Abu Hamza ya faɗa a lokacin da ya ke nuni da yatsun hannunsa jikin Motarsa kirar Akori-Kura, TOYOTA HILUX da ta yi matukar nuna gazawa.
A dai-dai lokacin Yagana tare da Kawarta Zaliha suka keto karshen Unguwar HINDAWIYYA, suka karaso yankin GANYARI wurin da BAKIN HAURE suka mai da shi tashar Motar zuwa kasuwar HARAJ ala tilas!
Ta daga Kafafunta yunkuri guda ta dira a bayan Motar Abu Hamza, wurin da a bisa al'ada aka tanada domin zuba Kaya.
Ta yunkura ta janyo hannunta, cikin nuna kwafa ta ce, "Na ga ranar da za ki wartsake ki saki jikinki, ki san cewa nan din inda ki ke wuri

ne da ya ke bukatar jarumta da jajurcewa ba lalaci ba". Yagana ta ce da Kawarta Zaliha.
Abu Hamza ya ci gaba da fadin;
"HADIT!
Haraj!! Haraj!!!"
Hadit!! Hadit!!!
HARAJ!
Yana sake maimaitawa har ma ya lura Motar ta cika fal! da Passenger Gaba Mutum biyu, Gidan Tsakiya wanda ya ke shima a rufe Mutum hudu.
Sai kuma Gidan Baya da ke dauke da Mutane har takwas. Kowanne ɓari na cin Mutum hudu.
Tsakiyar wurin kuma shake yake da kayan matafiya, waɗanda galibi Gumama ne (Tsofaffin Kayan Larabawa) da za a ci Kasuwar su anan Kasuwar Haraj.
Abu Hamza ya miki hanya ba tare ca wani fargaba ba, don kuwa yana da tabbacin hanya lafiya, tafiya ce da ba ta wuce ta tsayin kilo mita biyu ba.

A haka har suka iso Kasuwar Haraj, Abu
Ilamza ya karɓi hakkinsa Riyal biyu-biyu, sannan kuma ya yi nufin kama gabansa.
Da kyar! ta ke iya jan fagon kayan bugu guda, ga dai nauyi ga kuma tarin yawa. Yagana ta dubeta a hasale.
"Da zafi-zafi akan bugi karfe!"
Ko ba ki ji karin maganar da ku Hausawa ku ke fadi ba?
"A bari ya wuce kuma shi ke kawo RABON WANI!"
Ta finciketa hade da nata kana ta saɓesu a Kafadunta, Zulaiha na binta kamar Rakumi da Akala, suka kutsa cikin kasuwar Haraj har suka dangana da karshen kasuwar gefen hanya wurin da Takari suke baje kolin Hajarsu, daga nan aka shiga cin kasuwa ka'in-da na in.
Galibi baki daga kasashen (Africa) Afirka daban-daban ke cin kasuwar, wannan rukuni na kasuwar Haraj dama bakin haúre mazauna kasar da suka fito daga Nahiyar ta (Africa) Afirka

idan kuwa ta fannin masu ullata Ilajar ne 'yan kasar (Chad) Chadi sun yiwa kowa zarrah, kusan ma su suka fi cin gajiyar sana'ar.
Sun nutsa sako da lungunan Kauyukan Jiddah domin yin Barah, sukan baranto Kaya masu kyau su zo su kwalar da su a kasuwar ta Haraj.h
Wani nau'i kuma na Kasuwar Gumama da ke cikin Haraj, akan same su ne ana cikin Haraj. Cikin wata katafariyar Bola da hukumar tattara shara take yasar da ita anan, wani sa'in Sharar Gidajen Sa'udan ce, wani sa'in na Kantuna, Gidajen Abinci da kuma Kamfanunuwansu da dai sauransu.
Takari kan tone Bolar iyakar karfinsu da nufin samun rabo, ko ko mu ce dubi da kanka, domin kuwa sai dai ka tone ka duba iyakar iyawarka, ba domin ka rasa abin tsinta ba, kayane masu inganci da suka hada da Suttura, kayan Lantarki, Katakon Daki (Furnutures), Shimfidun daki (Carpet) Kai! wani sa'in abincin gwangwani, Nama, Kifi, sandararriyar Kaza

Wasunsu kuwa sun fi mai da hankali ne da tsintar Karafa da (Al-Minium) Alminiyom, (gwana-gwanen Lemo suka fi yawa), inda za su kai wurin masu siya da suma suka fito daga yankin Afirka a auna kilo-kilo a baka Kudin adadin kilonka.
Kilon baya wuce Riyal daya zuwa biyu. Da ya ke irin wadannan mutanen suna da Igama (Takardar izinin zama a kasar) sukan kai Kamfanunuwa su siya su ba su kudin.
Tana da tarin sa'a duk wani al'amari da ta saka a gaba ta kan yi kokarin ta gano bayansa, bata da kasala bare nuna gajiyawa.
Yarinya ce mai karsashi a wani lokaci ka ce ta hada jinsi da mutanen 6oye sabi da saurin motsi, kafin wani lokaci duk wani abu da suka zo da shi Haraj da ma wadanda suka yi Asubancin tsinta a bolar Haraj sun kare sai 'yan tsirari da amfaninsu ba shi da wani yawa suka yasar, duk dai cikin kwazo da juriyar Yagana.

ASUWA TA YI KYAU, saura dame? Mu wuce Italian Vera Pizza Restaurant mu yi guzurin Pizza Vera (Nadadden Burodi mai nama da kayan lambu a ciki) sannan mu ci Abinci mu wuce gida Hindawiyya ko ma kai hakarkarin mu kasa mu sami afuwa (Kasancewar tunda Asubahi ake sammakon fitowa).
Zaliha.
Yagana ta fada a lokacin da take duban
Ta kuma ja hannunta, taki kaɗabn ya sanar da su Vera Pizza Restaurant anan dai cikin kasuwar ta Haraj.
Gidan abinci ne da yake da matukar farin jini a idanun Bakaken Fata ga saukin farashi ga kuma galibi nau'in abinci ne da yake kamanceceniya da nasu.
Kusan koda yaushe kusan kowacce rana matukar sun tako Haraj anan suke cin abinci su kuma yi guzurin tafiya da shi.

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login