WATA FUSKAR CHAPTER 2

Mr Novel

  

13 May 2025

589

WATA FUSKAR CHAPTER 2

 


 

gidansu, tana da wayewa mai yawa a dalilin yan uwanta sun yi karatu ban da haka ma Babanta tsohon ma'aikacin Gwamnati ne, da• ya sha transfer daga wanan gari zuwa wancan, don haka ta samu damar zama a garuruwa daban-daban cikinsu kuwa har da jihar Legos daga canne ma ta zo wannan Makarantar karatu. Gwana ce kwarai wajen iya kwalliya irin ta 'yanmatan zamanin, wurinta na soma ganin (lense) wato yanar ido, wurinta na soma ganin farce da yanda ake sanya shi kullum takan sanya sutura ne ya dace da kalan idonta da kuma yanayin adonta, gata da gashin kai mai tsawo da gazar-gazar bai bata wuya wajen tajewa gashi ta lankwasa shi ta yanda duk taso abin shi sabanin nawa da ya ke wahalar da ni kwarai wajen gyarawa. Doguwa ce amma ba sosai ba fara ce sol har tana wani ja-ja-ja, haka nan ma'abuciyar sanya dogayen takalma ce, ni kam a wurina Karimatu Aliyu mai kyau ce ko da dai na ji wasu suna cewa wai ta iya kwaskwarima ne kawai. Ita kuwa Sakinah Adam itama wayaiyar ce sai dai akwai banbanci mai yawa a cikin irin wayewar tasu ta fito ne daga babban gida, irin gidajen nan da ake da mata uku zuwa hudu da 'yan uba masu yawan gaske maza da mata, irin gidajen auren da ake rayuwar mowa da bora inda 'ya'ya ke da zabi kan wanda suka fi so tsakanin uwa da uba ko ka ji yaran gida suna fadin ai kyale Babanmu kawai, in gaskiya za'a fadi ai adalci bai ishe shi ba, randa suka rangwanta mishi, su ce kyautawa ne bai yi ba in ta dauro ma ka ji suna cewa wai Mamansu tana barinshi ne kawai da Allah, irin gidajen da ake rayuwar kowa kanshi kawai ya sani babu taimakekeniya tsakanin yan uwa da yan uwa a mafi yawancin lokaci ma a kan son a ga gajiyawar

'yan wani daki, tanfar dai ba uba daya ne ya hada ba, tana da dabi'a ta fuskantar abu kai tsaye babu tsoro ko faduwar gaba, haka nan ba ta iya boye so ko ki. Wata kila dama can haka aka yi ta, watakila kuma saboda rayuwar da ta tashi ciki a gidan su itama ta yi Makarantun kwana kenan ta taba barin gida ga dukkan alamu kuma ta san wani abu kadan game da addini, ma'abuciyar tsabta ce da kyama, tana da yawan kwalliya sai dai kwalliyar tasu tasha ban ban da ta Karima, haka nan tana da dabi'ar raha da yawan zolaya da kuma ban dariya, amma duka sai ta ga dama.

Kai wurin nan matattara ce ta jama'a, Sakina ce ta yi wannan maganar cikin 'yar siririyar muryarta. Karima ta bata amsa a sanyaye don dukansu wasu irin muryoyi ne da su masu sanyi da dadin sauraro, ai sanin haka ne yasa na kawo mu na kuma yi mana odar wadannan ciye-ciye duk da tsadar su don ba zai yiwu mu zauna kawai muna zare ido cikin mutane ba tare da muna cin wani abu ba, kowa ma sai ya gane abinda ya kawo mu.

Gabana ya yanke ya fadi, lokacin da na tambayi kaina abinda ta ke nufi da kowa ma sai ya gane abinda ya kawo mu. Kadin in kai ga kokarin gane abinda kalmar tata take nufi, sai na ji ta ce, "Yin saurayi a nan wurin da ki ke gani ba karamin abu ba ne, don kowa ki ka gani a nan din to da zafin shi."

Sakina ta ce, "Ai naga alamar hakan." Cikin zuciyata na ce, na shiganga, kar dai a ce zuwa nan din muka yi don neman samari?

Tuni na soma zare ido ina waige-waige, tsakanin mutane ko zan tantance zafin nasu da ake magana akai.

Lokacin ne na fahimci kashi hudu cikin biyar din mutanen da ke wurin dukansu maza ne, suma 'yan daidaikun matan da na hanga tare da wasu su ke ga dukkan alamu kuma tafiyarsu daya ne. Mu kadai ne mu ke zaune mata zalla, alamar zaman kanmu muke yi.

Hankalina ya yi matukar tashi, lokacin da na kalli agogon Karimatu da ke daure a hannuna, idanuwana suka shaida tara da rabi na dare, ban taba yin dare irin wannan ba a waje, balle kuma ace a tsakanin maza masu yawa haka, na sake maida kallona wurin su Sakina, naga su kam babu abinda ya dame su, cin abincinsu suke yi a hankali, tanfar ba su son ya kare. A hankali na buda baki zan yi magana da sauri Karima ta ce min, "Don

Allah ki rage murya kar ki sa duk a waiwayo ana kallonmu, ke na yi-nayi da ke ki koyi tausa muryarki kin ki, kin barta a tsaye kikam kamar ta maza, murya mai *lushi ai ado ne wurin 'ya mace." Na yi shiru ina kallonta, na kasa furta abinda nake son fadi, don kar ace muryata ba ta tausu ba, can cikin zuciyata dai wai lokaci nake so in gaya mata in kuma tuna mata da dokar Makaranta, takwas ne zuwa takwas da rabi ake kulle get (Gate).

Hankalina ya kara tashi da na yi tunanin inda wani abu zai yi dalilin shigowar mahaifina, nan wurin ya ganni an ya zai yarda cewar ni ce? Kan ka ce meye wannan?

Sai kawai na ji zuciyata tana tunano min da wakar da mukan yi wa 'yanmata masu mu'amalla da maza, a lokacin da na ke gida in da muke kiran su, "mai wasa da mazà karya, tunda na ganta na raina..." har zuwa karshen wakar. Tuni zuciyata ta shiga tunanin yadda za ayi in fidda kaina daga wurin nan tunda su kam ban ga alamar suna da shirin tashi ba. Ina cikin tunanin tashi don barin wurin ne, idanuwana suka kai kan kyakkyawar jakar da ke kan cinyata nan take kuma na tuna da takalmanta da ke makale a kafafuna, takalman da ban taba sanya masu tsininsu ba, duk da bata lokacin da aka yi ana koya min tafiya da su, da kyar na iya isowa bakin titi ban cire su na rike a hannuna ba da dai na sani da nawa kayan na sako na bar na aron duk da kiran da Sakina ta yi musu da sunan lya ta dah, don haka Karimatu ta bani aron kayan sakawa, ita kuma ta ba ni takalmi da Jaka da kuma gyale kayan da ko kadan ban ji dadin amfani da su ba, daga su har takalman sun matse ni da kyar na ke iya numfashi ga mahadar kafata ta gaji ciwo take yi min, bata saba jin nauyi irin wannan ba.

Takurar da nake cikin ta kai matuka, don haka na zartar wa kaina da hukuncin yi wa Karimatu magana tunda ita ce jagorar tafiyar tamu maimakon kawai su ganni na mike na kama tafiya. A hankali sosai na bude baki na ce mata "ko zamu tafi ne? Dare ya yi ban da haka ma kuma na takura, ga shi cikina..." kan in karasa ta yi maza ta ce "Yau naga abinda ya ishen, cikinki? To gara tun wuri in gaya miki kwandala ba ni da ita balle mu shiga mota, da kafa kuma ba zai yiwu mu taka ba, gara ma kawai ki hakura ki danne ko ma mene ne, har mu samu wadanda za su yi mana magana mu bi su su rage mana don iyakar kudina na tattara na biya odar abincin nan." Gabana ya sake yankewa ya fadi, na shiga

zaro

idanuwana ina raba su tsakanin Karimatu da mutanen da take cewa cikinsu ne wasu za su kula mu, mu tashi mu bi su don rage hanya, mutanen da babu dangin iya bare na Baba a cikinsu.

Muryata tana rawa, kamar yanda jikin nawa ma rawan yake yi, na ce mata mu taka kawai da kafa ni zan iya tafiyar. Ta yi wani lallausan murmushi ta ce, "To me ya yi zafi haka shi ba wuta ba? Sakinah kuma kasake ta yi tana kallona, cikin mamaki da takaici ta ce

"Mu tafi da kafa ki ka ce?"

Yanayin da na gani a tare da su na ko in kula yasa ni sunkuyawa da nufin cire zankala-zankalan takalman da ke daure a kafata, na rike su a hannun dan in ji dadin ficewa daga wurin, in yi tafiya ta in koma

Makaranta.

Sunkuyawata ke da wuya, sai na ji an dora min wani sandararren hannu kan kafadata, da sauri na dago kaina don ganin waye mai hannun tunda bai yi min kama da tattausan hannun su Karima da na saba ji ba. Ina dagowa na shaki wani wari da zan iya cewa ya fi karfin na sigari, tuni kuma idanuwana suka kai kan gabjejen mutumin da ke tsaye a kaina yana wani irin murmushi da ke kara baiyanar da lalacewar hakoranshi saboda hayaki. Wayyo ni 'ya su, abin da na iya fadi kenan daidai lokacin da jikina ya dauki rawa, kaduwar da na yi ta wuce gaban magana, kan ka ce komai sai kawai na hangi wani kato cafke da hannun Karimatu tana kici-kicin kwacewa, shi kuwa yana fadin "haba ki shiru mana ya ya za ki ba da ni a gaban gayu? In mun je can ai daidaitawa lafiya lau zamu yi."

Na sake fadin waiyo ni 'yasu." Ban san yanda aka yi ba, ban san yanda aka yi na fidda kaina ba in ban da ganina kawai da na yi makale jikin wasu mutane da ke shirin barin harabar hotel din, alamar sun kammala abinda ya kawo su. Ina makale da su sai bari nake yi tanfar wacce ruwan sama ya daka.

"Ke mene ne haka?" Daya daga cikin mutanen ya yi tambayar cikin yanayin tsawa, don baiyanar da takaici.

"Wasu 'yan iska ne suka biyo mu.".

Sassanyar muryar Sakinah da na ji ta bayar da wannan amsa, ita ce ta fahimtar da ni cewar ba ni kadai ce na yi nasarar fitowa daga wurin ba.

"Wasu 'yan iska suka biyo ku, ku fa? Ku ba 'yan iska ba ne, mene ne? Ai daidai da ku ne su din, irin samarin da suka fi dacewa da ku kenan tunda haka ku ke so, abin da kụ ka zabarwa kanku ne ku ka samu, ku yi maza ku kauce ku bani wuri." Fadi hakan daidai yana nufin bude kofar motar don shiga. Waiyo ni

'yasu, na kara fadi saboda jin maganar tashi kaduwar da nake yi ta kara tsanani, ta yanda

ba na iya rike fitsarin da ya matse ni, na sake shi nan wurin a tsaye a jikina.

"Kuyi hakuri, kuyi hakuri, ku sauke mu." Karimatu ta yi maganar tana goge fuska alamar wai kuka ta ke yi.

"Haba 'yan iskan yara kawai da ku ke nema ku lalata kanku tun ba ku isa komai ba." Ya fadi hakan tare da jan tsaki "camon ku shiga mu tafi." Da sauri muka shige bayan motar wacce bai yiwuwa in tsaya kwatanta laushinta, kyanta da kuma kamshinta. Karo na farko da na taba shiga irinta cikin zuciyata na tuna nasihar da Inna ke yi min in zata aike ni wani wuri da zan shiga mota ban da shiga mota mai kyau, mota in ta cika kyau to ta satan mutane ce, na daga ido don kallon su Karima don in ga ko suma suna tsoron motar kamar yanda nake tsoronta, ina hada ido da Karima na gane ashe mistsike idon da take yi ba gaskiya ba ne kukan karya take yi, don kuwa tuni har ta wastsake tana ta fara'arta.

A hanya muna tafiya shi kuwa mafadacin mutumin nan wanda ba shi ke tuka motar ba, bai fasa fadan da yake yin ba. "Haka kawai

0 Comments

Leave a Comment

Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search


Recent Article
FOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
FOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
Read MoreFOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
REASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
REASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
Read MoreREASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read MoreStop doing these things if you don't want to damage your looks
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read MoreHEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read MoreSIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read MoreTHE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
WORST FOODS FOR BELLY FAT
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read MoreWORST FOODS FOR BELLY FAT
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read MoreMOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
WATA FUSKAR CHAPTER 2
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 2
GWARZON SADAUKI PART 4
GWARZON SADAUKI PART 4
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 4